Jump to content

Victor Attah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Victor Attah
Gwamnan Jihar Akwa ibom

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
John Ebiye (en) Fassara - Godswill Obot Akpabio
Rayuwa
Haihuwa Ibesikpo-Asutan, 20 Nuwamba, 1938 (86 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Efik
Harshen uwa Ibibio
Karatu
Makaranta Columbia University (en) Fassara
John F. Kennedy School of Government (en) Fassara
Columbia Graduate School of Architecture, Planning and Preservation (en) Fassara
Harsuna Turanci
Ibibio
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Masanin gine-gine da zane da ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Obong Victor Bassey Attah (an haife shi ranar 20ga watan Nuwamba, 1938). Shi ne Gwamnan Jihar Akwa Ibom a Najeriya daga 29 ga watan Mayu shekarar 1999 zuwa 29 ga Mayu 2007.Ya kasance mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, amma daga nan ya koma jam’iyyar All Progressives Congress.

An haifi Obong Victor Attah a ranar 20 ga Nuwamba 1938.Ya kammala karatun gaba da firamare a shekarar 1956.Ya sami digiri daga Kwalejin Fasaha ta Leeds da difloma a fannin Kimiyyar Gine-gine daga Jami'ar Liverpool a 1965.Ya samu gurbin karo karatu a Jami’ar Columbia da ke New York,inda ya sami digiri na biyu a Advanced Architectural Design and Planning.Ya kuma halarci Makarantar Gudanarwa ta Kennedy a Jami'ar Harvard .Bayan ya kammala karatunsa,ya yi aikin gine-gine a yankin Caribbean,New York City,da Najeriya.Ya taba zama Shugaban Cibiyar Fasaha ta Najeriya ta kasa.

Gwamnan Akwa Ibom

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance daya daga cikin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Shehu Musa 'Yar'aduwa a cikin shirin mika mulki ta Sani Abacha da aka soke tare da 'yan siyasa irinsu Atiku Abubakar,Abdullahi Aliyu Sumaila,Magaji Abdullahi,Chuba Okadigbo da Sunday Afolabi.An zabi Victor Attah a matsayin gwamnan Akwa Ibom a shekarar 1999 a dandalin PDP na Akwa Ibom,kuma an sake zabe a shekarar 2003.An zabe shi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya 36 a shekarar 2003.

A cikin 2001,Attah ya yi tafiya zuwa Amurka tare da mutane kusan 21 don neman masu saka hannun jari na kasashen waje.Wannan ziyarar da sauran su sun samar da sakamako na gaske. Ya yi alkawarin inganta hanyoyin sadarwa, samar da wutar lantarki,da hanyoyin sufurin jiragen sama,da kuma yin kwafin Silicon Valley a Uyo.Ya shirya gina filin jirgin sama a Uyo kafin ya bar ofis a 2007. Ya aza harsashin kafa Jami’ar Fasaha ta Jihar Akwa Ibom.

Attah ya tsaya takarar neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party a shekarar 2007,amma daga baya ya janye.

Daga baya aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Obong Victor Attah ya yi ritaya daga siyasa bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2007.Ya kasance tare da matarsa Alison da ke fama da ciwon sukari na 2.

A cikin Maris 2008,Victor Attah ya shiga ExecutiveAction,mai ba da shawara wanda ke taimaka wa kamfanoni sarrafa matsaloli a cikin mawuyacin yanayin kasuwanci.

A ranar 24 ga watan Nuwamba,2018,a wata sanarwa da gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya fitar, ya sauya sunan filin jirgin sama na Akwa Ibom zuwa filin jirgin sama na Victor Attah,sunan tsohon gwamnan ne domin karrama shi saboda kasancewarsa wanda ya kafa filin tashi da saukar jiragen sama yayin da yake rike da shi.yayi mulki daga 1999 zuwa 2007.

  • Jerin sunayen gwamnonin jihar Akwa Ibom