Jump to content

Jinin Haida

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jinin Haida
biological process (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na menstruation (en) Fassara
Facet of (en) Fassara human reproduction (en) Fassara da women's health (en) Fassara
Found in taxon (en) Fassara Homo sapiens (en) Fassara
Described at URL (en) Fassara bacsisaigon.net… da bacsisaigon.net…
WordLift URL (en) Fassara https://data.thenextweb.com/tnw/entity/menstruation

Jinin Haida((حيض)) to muna farawa da sunan Allah mai Rahma mai Jinkai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya.[1][2] Bayan haka ga wasu daga abinda ya shafi hukunce-hukuncen jinin al'ada wanda ake kira Jinin haida, yana da matukar muhimmanci sanin hukunce-hukuncen jinin al'ada, muhimmancin ba wai ya tsaya ga mata bane kadai a'a har da maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada, misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a sakinta idan Kuma aka yi sakin to ya tabbatar, ba kuma a saduwa da ita, sannan ga yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku (al'ada uku) kafin aka ce ta kammala iddah sannan ai maganar sabon aure, to idan tana al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan sai bayan shekara daya da rabi za'a fara maganar aure, shi ya sa muka ce sanin hukunce-hukuncen wannan jinin ba wai ya rataya ga mata bane kadai har da maza.[3][4].

Masana sun kayyade cewa lafiyayyen jinin al'ada yakan shafe kwanaki huɗu (4) zuwa kwanaki bakwai (7) yana zuba sannan ya dauke, idan ya dauke yakan shafe kwanaki ashirin da daya (21) zuwa kwanaki talatin da biyar (35) kamin kuma ya sake [1].[5]

Menene Jinin Al'ada

[gyara sashe | gyara masomin]

Jinin al'ada jini ne da yake fita da karan kansa daga gaban macan da a al'adance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce kwanaki goma sha- biyarba. Wannan shi ake nufi da jinin al'ada, da aka ce 'jinine da yake fita da kansa' kenan idan ya zamana ba da kansa ya fita ba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinin ya balle mata to wannan bai zama jinin al'adaba. Da aka ce 'Ta gaba' kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al'adaba. Da aka ce wacce a al'adance zata iya daukar ciki kenan idan ya fita daga wacce a al'adance ba zata iya daukar ciki ba sabo da yarinta ko girma to wannan shi ma bai zama jinin al'ada ba. Amma da aka ce 'Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha biyar ba, kenan idan ya wuce kwanaki sha biyar (15) to bai zamo kuma jinin al'adaba. Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin al'ada ba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau kansu ba za su yi sallah domin jinin ciwo ne sai a nemi magani, Allah ya sawwake.

Mafi Karancin sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Malamai sun karawa juna sani kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa shi ne dugo guda ɗaya kenan idan ya ɗiga sannan ya ɗauke, shi kenan ta yi al'ada kuma ta dauke.

Mafi Yawansa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mafi yawan kwanakin jinin al'ada shi ne kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya wuce haka to bai zama jinin al'ada ba muddin ba ciki take da shiba. Mata Dangane da Al'ada: anan mun sani mata suna da halaye biyar musamman idan muka yi la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya zo na al'adane ko bana al'ada ba ne, kamar haka:

  1. Kasa da shekara tara Idan jinin ya

zo wa yarinyar da take kasa da shekara tara to malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada ba ne, jinin ciwo ne sai a nemi magani.

  1. Tara Zuwa Sama Idan ya zamana jinin ya

zo ne ga wacce ta cika shekara tara zuwa zamanta budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin na al'adane ko na ciwo. Kada mu sha'afa yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da hutu da wahala suna tasiri.

  1. Budurci Zuwa Sheka 50 Idan jinin ya

zo daga lokacin da ta zama budurwa zuwa shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.

  1. Daga 50 - 69 Idan jini ya zo wa mace

a tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai suka ce za'a tambayi kwararrun mata da likitoci domin sanin wannan jinin na ciwone ko na al'ada.

  1. Daga 70 Idan jini ya zo bayan mace ta

cika shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai suka ce wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane. Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce-hukunce a kansu, kuma ana gini ne a kan tsarin kalandar musulunci, wadannan bayanai na karkasuwar mata har zuwa gida biyar kamar yadda ya gabata haka malam Adawi ya kawo a cikin littafinsa 'Hashiyatul Adawi', Allah ya ji kansa da gafara. Ina daɗa jaddada cewa yanayin abinci da da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri matuka, dukkan abinda ba'a fahimta ba dangane da yana yin zuwan jinin ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi bayai da cewa yana da alaka da hukunce-hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da aka saka zata iya kammala idda akasa da watanni uku. Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shi ne zuwansa na farko sannan ya tabbata cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga, dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta mata lada idan kuma ta bari samari suna jagwalgwalata ita za'a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka wanda ta sha.

Tabbatuwar Jinin Al'ada

[gyara sashe | gyara masomin]

Shifa abin da ya shafi jinin al'ada al'amari ne da Allah maɗaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa: Kuma suna tambayarka dangane da al'ada, Kace: Shidinnan cutane, ku nisanci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka. Bakara, ayata: 222. Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- yace; (Wannan) Wani abu ne da Allah ya dorawa mata 'ya'yan Adam. Ashe ba shaci-fadin da ake cewa ba ne ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shi ne wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi ya sa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar. Shi fa jinin al'ada kada amanta jini ne da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya zama abinci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai,sa Allah ya sanya shi ya zama abinci gareshi,shi ya sa da kyar ka ga mace tana da juna biyu (ciki) kuma tana al'ada. Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi nono jaririn yana sha amatsayin abinci,shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya kasance ba inda zai je to shi ne sai ya taru a mahaifarta,shi ne mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah- gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.

wannan yadda jinin al'ada yake kwarara kenan daga jikin wata baturiya

.

Karkasuwar Mata

[gyara sashe | gyara masomin]

Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; ita ce wacce ta fara, kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka:

digon Jinin al'ada
  1. Wacce Ta Fara Ita wacce ta fara

al'ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwarta, to abin da yake kanta zata zuba ido ne ta ga kwanaki nawa zai dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyar ba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'ada ba, kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Istihadha) cuta sai a nemi magani, anan nake cewa iyaye su kara sa ido a kan 'ya'yayansu mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka, wata babbar mace ce amma bata san menene jinin al'ada ba ita dai kawai ta ce tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.

  1. Wacce Ta Saba' Abinda ake nufi da

wacce ta saba ita ce wacce ta gabatar da al'ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shi ma kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da tsayayyun kwanaki.[6] Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al'ada to wadannan kwanakin su ne kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada da kuma sauran mu'amaloli na zamantakewar ma'aurata, amma idan kwanakin suka cika al'adar kuma bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki shabiyar su cika, misali idan al'adarta kwanaki biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki biyar din ba sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shi kenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara uku sun zama sha hudu idan bai daukeba sai ta kara kwana daya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai daukeba domin kwanakin al'ada makurarsu shi ne kwana goma sha-biyar kuma sun cika, abin da ya ci gaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada ba sunanshi jinin cuta (Istihadha) sai a nemi magani, dukkanin wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta Kara kwana uku na saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin ukun shi kenan sai ta yi wankan tsarki. Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha- biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

  1. Mai Juna-biyu (Mai ciki) Galibin mata

masu juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita . Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan ana da juna biyu kuma aka ga jini. Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda zata yi anan shi ne, ta tsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki domin da hakane zata cika kwanakinta na al'ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to na biyun zai zama sabon jini ne kenan, ba na da ne ya dawo ba. Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jinin al'ada ya dauke akwai alama da shara'a ta sanya domin ya zama shi ne manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:

  1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan

shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata al'adarta ta dauke.

  1. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari

mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta kammala. Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba ganin al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfa ba, amma idan wacce ta saba gani ce sai ta ga bushewar gaba to malamai sukace zata zata dan saurara kadan domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba. A dunkule dai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci guda ba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin ya dauke mijinta ba zai sadu da ita ba kuma ba zata yi sallah ba, da dai sauransu. Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jini ne, amma idan a karshen jini ne to wannan ba komai, Ummu Atiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) tace: ((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi- fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abu ne)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368, Ibnu Majah Hadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865. Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba a ce ta tashi cikin dareba domin ta duba. Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da la'asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi sallar magariba da lisha. Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai- al'adaba: Anan za'a lissafa abubuwan da basu halatta mai al'ada ta yi su ba ko ayi mata ba, wadannan abubuwane guda goma:


1. Sallah: Bai halatta mai al'ada ta yi sallaba farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yi ba'akarba ba sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta kammala al'adar ba zata rama sallolinba.


2. Saki: Baya halatta matar da take al'ada a saketa, wannan ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka koda yana son ya saketa to ya bari sai ta kammala al'ada kafin ya sadu da ita sai ya saketa, kuma dai idan ya saketa tana jinin al'adar to sakin ya yi amma za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai ukuba.


3. Dawafi: Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.


4. Zama A Masallaci: mai al'adah ba zata zauna a cikin masallaciba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.


5. Azumi: Bai halatta mai al'ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo, amma dazaran ta zo to dazaran ba azumi, dazaran bata zoba to dazaran akwai azumi, ko da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.


6. Daukaa Alkur'ani: mai al'ada bata dauka Alqur'ani kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.


7. Karatun Alkur'ani: mai al'ada bata karanta Alkur'ani, dudda cewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi da ka domin kada ta manta sabanin dauka.


8. Saduwa: Bai halattaba saduwa da mace tana al'ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa Allah ba asalima ta yi biyayyane ga reshi, bai halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al'adar ta dauke amma batayi wankaba to bai halatta a sadu da itaba. Ya halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa alokacin da take al'ada bayan ta yi kunzugu inbanda daga cikbiyarta zugwiwarta wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.


9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al'ada tana tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.


10. Wajabta Wanka: Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta. Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al'ada bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba, kuma lalle idan aka kyalleshi yadda ake sakaci tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi wannan al'amari to lalle abin yanada ban tsoro.

Allah ya datar damu yasa mu dace. Allah shine mafi sanin masu sani.

  1. Basheer Ridwan, Muḥammad (10 July 2016). "ALAMOMIN ƊAUKEWAR JININ HAILA !". Darurfikr.com. Retrieved 10 August 2021.[permanent dead link]
  2. https://m.facebook.com/SheikhJafar.Org/posts/924760954314729
  3. https://m.facebook.com/permalink.php?story_fbid=363012365086682&id=100212108033377
  4. "Jinin Haila: Abubuwan da suka kamata ki sani kan al'ada da daukar ciki". bbc hausa. 16 August 2020. Retrieved 10 August 2021.
  5. https://www.lafiyata.com.ng/2023/01/rikicewar-alada-jinin-haila-da-kuma.html?m=1
  6. https://sunnahmedianigeria.wordpress.com/2015/04/01/9795999/